26 Disamba 2021 - 18:22
Ibrahim Ra'isi: Atisayan Da Dakarun Kare Juyin Na Kasar Suka Yi Alama Ce Ta Karfin Tsaro

A wani bayani da ya fitar a sakon tayar murnar zagayowar ranar Haihuwar Annabi Isa As Ibrahim Ra’isi shugaban kasar iran ya fadi cewa Atisayan da dakarun Karen juyin musulunci na Iran suka yin a Rasulul Akram na 17 yana nuna karfin tsaro da kare kai da iran ake da shi ne.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ana sa bangaren shugaban majalisar kolin tsaron kasa ya yaba game da kokarin da dakarun kare juyin suka yi wajen gudanar da Astiyan rasulul akram na 17 cikin nasara , yace Aitisan mai cin dogon zango wata Alama ce ta karfin tsaro da iran take da shi wajen kare kasar, kuma duk wani gigi da makiya za su yi to zai fuskanci mayar da martani mai zafi ,

A ranar 20 ga watan Decembar da muke ciki ne aka kaddamar da Atisayan Rasulul Akram na 17 a tekun fasha da mahsiagr Hurmuz da bushahar da yankin KHuzistan kuma aka kammala a ranar juma’a 24 ga watan Decemba inda aka baje kolin manyan makaman kare da dakarun ska kera a cikin gida.

342/